IQNA

Musulmin Nageria Sun Nuna Rashin Amincewa Da Dokar Hana Saka Hijabi

23:56 - July 15, 2015
1
Lambar Labari: 3328728
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci a tarayyar Najeriya sun nuna rashin gamsuwarsu da matakan da ake dauka na hana mata saka hijabin musulunci saboda dalilai na tsaro.


Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Anatoli cewa, Khalid Abubakar shugaban kungiyar Jama’at Nasr Islam, ya ce mabiya addinin muslunci a kasar suna nuna rashin amincewarsu da gamsuwarsu da matakan da ake dauka na hana mata saka hijabin musulunci a kasar.

Ya ce jami’an tsaro suna fakewa da batutuwa na tsaro wajen hana mata saka hijabi wanda addininsu ya yarje musu da su saka, amma kuma wannan ba zai taba zama dailai na takura mata musulmi ba, akan haka suna kira da a sake yin nazari kan wanann batu.

Mahukunta a bangaren tsaro a tarayyar Najeriya sun bayyana cewa suna daukar matakai na tababtar da tsaro, da hakan ya hada binciken mata wadanda akan yi amfani da su wajen tayar da bama-bamai a kasar, wada kuma hakan yana faruwa ne ta hanyar saka hijabin muslunci.

Da dama daga cikin kungiyoyin mabiya addinin muslunci a kasar dai sun mike tsaye wajen ganin cewa hakan bai zama wata hanya ta cin zarafin mat aba, tare da neman mahukunta da su duba wannan lamari domin samun fahimtar juna.

Adadin mabiya addinin muslunci a tarayyar najeriya sun kai kashi 55 cikin dari, yayin da kuma mabiya addinin kirista sun kai kashi 40, sauran kuma suna kan wasu hanyoyi na addinan gargajiya da sauransu.

3328373

Abubuwan Da Ya Shafa: nigeria
Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
hamadou ali lete nijar
0
0
ay mata wonda ya rike da sunan annabi s a w ba zay fita ba ko a tche woni hijdabi
captcha