IQNA

Kur’ani Shi Ne Tushen Dukkanin Ilmomin Ci Gaban Dan Adam

21:19 - October 13, 2015
Lambar Labari: 3385197
Bangaren kasa da kasa, Abdulganiyi Oladuso malamin jami’ar Ilorin a Najeriya ya bayyana cewa kur’ani mai tsarki shi ne tushen duk wani ci gaban ilimin dan adam.


Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Naija247 cewa, Abdulganiyi Oladuso malamin jami’a a Najeriya ya bayyana kur’ani mai tsarki da cewa shi ne babban tushen ilmomi na ci gaban bil adama a kowane zamani.

Ya bayyana hakan ne a zantawarsa da wasu manema labarai, inda y ace amfanin ilimi shi ne a amfanar da mutane da shi.

Oladuso ya ci gaba da cewa, wajibi ne a kan musulmi da su ci gaba da kara bunkasa a iliminsu domin sai da ilimi ne ake samun ci gaba ta kowace fuska, kuma sai da shi ne ake samun ilimin kusanci da ubangiji madaukakin sarki.

Haka nan kuma ya kara jadda muhimamncin neman ilimi a dukkanin bangarori, da hakan ya hada da addini da kuma na zamani wanda zai taimaka ma mutum a rauwarsa.

Abdulganiyi Abdulsalam Oladuso malami ne jami’ar Ilorin a Najeriya, kuma yana koyar da harshen larabci, kamar yadda kuma yake gudanar da wasu ayyuka da suka shafi kur’ani mai tsarkia  kasar.

3385012

Abubuwan Da Ya Shafa: nigeria
captcha