IQNA

Gangamin Masu Adawa Da Kulla Alaka Da Isra'ila

22:57 - October 17, 2017
Lambar Labari: 3482008
Bangaren Kasa da kasa, wasu gunun masu adawa da kulla da alaka da Isra'ila akasar Bahrain sun gudanar da gangamin nuna rashin amincewa da masarautar kasar na neman hada kai da yahudawa.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya ahbarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Manama Post cewa, wasu gunun masu adawa da kulla alaka da Isra'ila akasar Bahrain sun gudanar da gangamin nuna rashin amincewa da masarautar kasar na neman hada kai da yahudawan haramtacciyar kasar Isra'ila.

Bayanin ya ci gaba da cewa, babban dalilin da yasa wadannan mutane suka kirkiri wannan gangami shi ne nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu da kuma gwagwarmayar da suke yi wajen neman hakkokinsu da yahudawa suka danne musu.

Dangane da yunkurin da masarautar mulkin kama karya ta Bahrain ke yin a neman dawo da alakar diflomasiyya a hukumance a kasar kuwa, gungun ya nuna cewa wanann cin 

amanar al'ummar Palastinu da sauran al'ummomin larabawa da msuulmi ne.

Gwamnatin kama karya ta Bahrain dai tana da kyakyawar alaka tare da gwamnatin yahudawan sahyuniya, kuma suna gudanar da dukkanin harkokinsu a bayyane, duk da cewa a hukunamce babu alaka tsakaninsu, amma kuma akwait a aikace.


3653691

captcha