IQNA

MDD Ta Dora Laifin Kisan Musulmin Rohingya A Kan Gwamnatin Myanmar

23:38 - October 19, 2017
Lambar Labari: 3482015
Bangaren kasa da kasa, majalisar dinkin duniya ta dora alhakin kisan musulmin Rohingy a akan gwamnatin kasar Myanmar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, kafanin dillancin labaran Faransa ya habarta cewa, masu bayar da shawara na musamman ga babban sakataren majalisar dinkin duniya sun bayyana cewa, gwamnatin Myanmar ce ke da alhakin kisan ‘yan kabilar Rohingya.

A cikin bayanin rahoton da suka gabatar, sun bayyana cewa tun kafin wannan lokaci akwai alkawullan da gwamnatin Myanmar ta dauka na ganin cewa ta kare rayukan musulmi ‘yan kabilar Rohingya marassa rinjaye a kasar, amma bata yi aiki da ko daya daga cikin wadannan alkawulla ba.

Daga watan Agustan da ya gabata ya zuwa yanzu, fiye da mutane dubu 500 ne musulmi ‘yan kabilar Rohingya suka tsere zuwa cikin kasar Bangaladesh domin tsira da rayukansu daga kisan kiyashin da jami’an sojin gwamnatin Myanmar tare da masu addinin buda ke yi a kansu.

Rahotannin da majalisar dinkin duniya ta harhada tare da kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya, sun tabbatar da cewa abin da aka aikata akasar laifine na kisan kiyashi a kan ‘yan kabilar Rohingya marassa rinjaye.

3654593


captcha