IQNA

An Bukaci A Gudanar Da Bincike Kan Batun Hana Wata Daliba Saka Hijabi A Najeriya

22:49 - February 07, 2018
Lambar Labari: 3482374
Bangaren kasa da kasa, wasu kungiyoyin musulmi sun bukaci babbar kotu a Najeriya da ta gudanar da bincike kan batun hana wata daliba saka hijabi.

 

Kamfanin dillancin labaran iqn aya ahbarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na PMNews Nigeria cewa, kungiyoyin musulmi sun bukaci babbar kotu a Najeriya da ta gudanar da bincike kan batun hana wata daliba saka shahadar kammala karatun lauya sakamakon saka hijabin musulunci.

Bayanin y ace kungiyoyin sun bukaci kotun da ta yi bincike na gaskiya tare da daukar matakai na kawo karshen irin wannan aiki, wanda ya yi hannun riga da dokokin da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar.

Kotun ta fara gudanar da bincike kan wannan batu a ranar 5 ga watan Fabrairu kuma za a ci gaba da bincike kan batun domin gano hakikanin abin da ya faru.

Bayanai sun yin nuni da cewa an matar wadda ta kammala karatun lauya shiga wurin taron yaye daliban da suka kammala karatun ne bayan da ta saka lullubi a kanta, wanda shugabannin taron suka bayyana hakan da cewa ya sabawa kaida, a kan haka aka hana ta takardar shedar kammala karatu.

3689436 

 

 

captcha