Kamfanin dillancin labaran iqna ya habart cewa, gwamnatin kasar ta Masar ta ta samu nasarar dawo da tsohon kwafin kur’anin ne mai rubutu da ake ake kira Atlas Susman Saidid, bayan fitar da shi daga kasar na tsawon shekaru zuwa kasar Jamus.
An dawo da wannan kafin kur’anin ne bayan da mutumin da yake mallakarsa a kasar ta Jamus ya fitar da shi domin sayarwa, inda ma’aikatar kula da harkokin al’adu ta kasar Msar ta gagauta domin fansarsa.
Wannan kwafin kur’ani an fanshe shi ne akan kudi yuro dubu ashirin da shida, kuma yanzu haka an dawo da shi kasar Masar, tare da hadin gwiwa da gwamnatin Jamus.