IQNA

Adadin Malaman Kur’ani Maza Ya Ragu A Kasar Aljeriya

23:52 - October 21, 2018
Lambar Labari: 3483061
Bangaren kasa da kasa, wani bincike da aka gudanar a kasar Aljeriya kan adadin malaman kur’ania  kasar ya nuna cewa addain malaman kur’ani maza ya ragu.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na Albawwabah News cewa, bisa wani bincike da wata cibiyar bincike ta  gudanar a kasar Aljeriya, kan adadin malaman kur’ani maza da mata a  kasar, ya nuna cewa addain malaman kur’ani maza ya ragu idan aka kwatanta da mata.

Saikamakon binciken ya nuna cewa adadin maza masu koyar da kur’ani a makarntu kama daga na zamani har zuwa na gargaji ko kuma na allo, ya nuna cewa adadin ya ragu idan aka kwatanta da loktan baya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da adadin mata masu koyar da kuyr’ani makarantu ya karu fiye da kowane lokaci a tarihin kasar.

Wannan lamari ya sanya cibiyoyin kur’ani suka fara tunanin gano dadlilan da suka jaza hakan, musamman ma ganin cewa mafi yawan daliban da makarantunsuke yayewa musamman wadanda suka yi karatu mai zurfi maza ne.

3757476

 

 

 

 

captcha