Kamfanin dillancin labaran iqna,
Ma’ikatar kiwon lafiya a kasar Sudan ta sanar ad adadi na karshe na wadanda suka rasa rayukansu a zanga-zangar da aka gudanara kasar wadda ta kawo karshen mulkin Albashir.
A cikin bayanin da ta fitar a jiya, ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Sudan ta sanar da cewa, mutane 53 aka tabbatar da mutuwarsua dukkanin fadin kasar, a zanga-zangar kin jinin gwamnatin hambararren shugaban kasar ta Sudan Umar Hassan Albashir.
Bayanin ya ce mafi yawan mutanen sun rasa rayukansu ne a yayin zanga-zangar, biyo bayan artabun da aka yi tsakaninsu da jami’an tsaro, yayin da kuma wasu suka rasu a asibiti sakamakon samun munanan raunuka.
Jami’an tsaron sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa masu zanga-zangar, musammana biranan Khartum da kuma Ummu Durman, da wasu yankuna a cikin Darfur.