IQNA

Gwamnatin Sin Ta Tsananta Matakai Na Takura Wa Musulmin Kasar

23:50 - July 08, 2019
Lambar Labari: 3483820
Bangaren kasa da kasa, Wasu ‘yan kasar China masu fafutuka sun zargi gwamnatin kasar da kara tsananta matakan da take dauka a kan musulmin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga jaridar Daily Sabah cewa, a jiya ne musulmin kabilar Igor na kasar China suka gudanar da taron cika shekaru goma da fara boren da suka yi, kan cin zarafin da ake yi musu a cikin kasarsu.

Shugaban kungiyar kare hakkokin musulmi ‘yan kabilar Igor a kasar China Sit Tomturk ya bayyana cewa, irin matakan da gwamnatin kasar take dauka a kansu, yunkuri na share duk wata al’ada ta musulunci a yankin nasu baki daya.

Ya ce yankin Sin Kiyang yanki ne da ke musulmi fiye da miliyan goma, amma fiye da miliyan biyu daga cikinsu suna tsare a kurkuku a cikin mawuyacin hali.

Ya ci gaba da cewa sun yi bore ne a cikin shekara ta 2009 sakamakon takura da hana su gudanar da harkokin addininsu kamar yadda ya kamata, inda jami’an tsaron gwamnatin China suka yi amfani da karfi wajen kashe adadi mai yawa na muuslmin yankin.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da dama a duniya dai suna sukar gwamnatin kasar China, sakamakon matakan takura wa musulmin kasar da take dauka.

 

 

 

 

3825031

 

 

 

captcha