IQNA

Kungiyar OIC Za Ta Gudanar da Zaman Gaggawa Kan Isra’ila

23:49 - July 15, 2019
Lambar Labari: 3483843
Kungiyar kasashen musulmi ta kirayi zaman taro na gaggawa dangane da irin sabbin matakan Isra’ila take dauka a cikin kwanakin nan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da kungiyar kasashen musulmin ta OIC ta fitar, ta bayyana cewa dole a dauki matakan gaggawa domin takawa Isra’ila brki dangane da irin take-takenta.

Kungiyar ta ce a cikin wannan makon mai kamawa za ta gudanar da zaman taro tare da halartar wakilan dukkanin kasashen musulmi, domin tattauna halin da ake ciki a Palestine, kan irin matakan da Isra’ila take dauka na mamaye wasu yankunan falastinawa a gabashin birnin Quds, .

Baya ga haka kuma taron na OIC zai dubi kan shirin Isra’ila wanda ta fara aiwatarwa, na gina manyan ramuka a karkashin masalalcin Quds mai alfarama, wanda hakan zai iya yin sanadiyyar ruftawar masallacina  kowane lokaci.

Tun daga cikin shekara ta 1967 ce Isra’ila ta mamaye yankunan falastinawa a cikin birnin Quds, kuma take ci gaba da kara fadada mayar yankuann a kowane lokaci.

 

 

3827216

 

 

 

captcha