kamfanin dillancin labaran iqna, a, kasar Tunisia a jiya Asabar ne akayi jana’izar shugaban kasar Béji Caïd Essebsi, wanda Allah, ya yi wa rasuwa a ranar Alhamis data gabata, yana mai shekaru 92 a duniya.
Daga cikin wadanda suka halarci jana’izar, har da shugaban kasar faransa, Emanuel Macron, da shugaban Palasdinawa Mahmud Abass, da shugaban gwamnatin hadin kan kasa ta Libiya Faez Al’Saraj, da sarkin Qatar,
Mirigayi Béji Caïd Essebsi dan ashekaru 93 a duniya, shi ne wani shugaban kasa na farko a Tunisia da aka zaba ta hanyar demokuradiyya, bayan guguwar neman sauyi da ta kawo karshen tsohuwar gwamnati.