IQNA

An Kasa Cimma Wata Matsaya A Tattaunawar Sulhu Da Taliban

20:04 - November 20, 2018
Lambar Labari: 3483141
Manzon musamman na Amurka da ke shiga tsakani a tattaunar sulhu da kungiyar Taliban, ya kasa shawo kan mayakan kungiyar kan su rungumi tafarkin zaman lafiya.

Tashar talabijin ta euro news ta bayar da rahoton cewa, a tattaunawar da ta gudana a tsakanin Zalmai Khalil Zad manzon musamman na Amurka da ke shiga tsakani a tattaunar sulhu da kungiyar Taliban, da kuma wqakilan kungiyar, an tashi ba tare da cimma wata matsaya ba.

Kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya bayyana cewa, a cikin tattaunawar da ta gudana tsakaninsu da manzon musamman na Amurka, babu wani abu da aka iya cimma matsaya a kansa a tsakanin bangarorin biyu.

Kungiyar Taliban ta fusata ne bayan furucin da Zalami Khalilzad ya yi ne kafin fara tattaunawar, inda ya ce ya kamata kungiyar Taliban ta kwana da sanin cewa ba zata taba yin nasara ta hanyar daukar matakai na soji ba.

An gudanar da zaman tattaunawar ne a birnin Doha na kasar Qatar tsawon kwanaki uku a jere, wanda aka kammala a jiya Litinin.

3765709

 

 

 

 

 

captcha