IQNA

Mutanen Afirka Ta Kudu Na Neman Gwamnati Ta Rufe Ofishin Jakadancin Isra’ila

22:48 - May 31, 2021
Lambar Labari: 3485967
Tehran (IQNA) Dubban mutane ne suka gudanar da jerin gwano a kasar Afirka ta kudu domin yin kira ga gwamnatin kasar da ta rufe ofishin jakadancin Isra’ila.

A rahoton kamfanin dillancin labaran Iqna, a jiya mutane da dama ne suka gudanar da wani jerin gwano na lumana a birnin Limpopo na kasar Afirka ta kudu, domin yin kira ga gwamnatin kasar da ta rufe ofishin jakadancin Isra’ila da ke birnin Pretoria.

Jerin gwanon wanda an shirya shi ne domin jaddada goyon baya ga al’ummar Falastinu, da kuma yin Allawadai da salon mulkin zalunci da wariya na Isra’ila a kan al’ummar Falastinu, wanda kungiyoyin farar hula gami da kungiyoyin kare hakkin bil adama, da masu adawa da mulkin wariya ne suka shirya gangamin.

Daya daga cikin mambobin majalisar mayasa ta kasar Afirka ta kudu, wanda yana daya daga cikin wadanda suka shirya jerin gwanon ya bayyana cewa, suna yin kira da babbar murya ga gwamnatin kasar Afirka ta kudu, da ta gaggauta daukar matakin rufe ofishin jakadancin Isra’ila da ke kasar.

Ya ce ba za su amince da ofishin jakadancin kasar da nuna wariya tsakanin ‘yan adam ba, tare da yi musu kisan kiyashi da kuma haramta musu hakkokinsu a cikin kasarsu, wanda a cewarsa wanann shi ne abin da al’ummar Afirka ta kudu ta yi fama da shi a baya, shi ne kuma Isra’ila take aikatawa kan Falastinawa.

 

3974630

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: falastinawa
captcha