Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, da farko ‘yan bindigan sun kwace iko da ofishin ’yan sanda na garin sannan suka yi ta harbi a sama don tsoratar da mutane kafin su shiga wata makarantar islamiyya su tafi da wasu ‘yan makaranta.
Labarin ya nakalto shugaban makarantar Malam Yakubu Idris ya na cewa ba’a san adadin daliban da suka tafi da sub a, amma sun tafi da diyarsa.
Amma makarantar tana da daliban nusary da Firaimaresannan da yamma kuma da karshen sati suna karantar da addini a cikinta.
Garin Tegina dai shi ne garin shugaban karamar hukumar ta Rafi a jihar ta Niger Isma’ila Modibbo, yanzu haka dai jami'an tsaro suna suna cikin sintiri da bin kadun lamrin.