IQNA

Taron Kara Wa Juna Sani Na Kasa Da Kasa Dangane Da Marigayi Imam Khomeini

22:58 - June 01, 2021
Lambar Labari: 3485971
Tehran (IQ) za a gudanar da taron karawa juna sani dangane mahangar marigayi Imam Khomeini a daidai lokacin tunawa da zagayowar lokacin rasuwarsa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, cibiyar kula da ayyukan bincike kan rayuwar marigayi Imam Khomeini, za ta shirya gudanar da taron karawa juna sani dangane mahangarsa a kan lamurra da dama da suka shafi duniyarmu ta yau.

Taron wanda zai gudana ranar Alhamis mai zuwa a hubbarensa da ke birnin Tehran, zai samu halartar baki daga ciki da wajen kasar, wadanda za su gabatar da jawabai a wurin.

Shekaru talatin da biyu da suka gabata a rana irin ta yau marigayi Imam Khomaini ya rasu yana dan shekara 87 a duniya.

An haifi Imam a ranar ashirin da biyu ga watan Satumban shekara ta  alif da dari tara da biyu a garin Khomain da ke tsakiyar kasar Iran.  ya fara karatu a gaban mahaifinsa, bayan rasuwarsa kuma babban yayansa ya ci gaba da koyar da shi.

Imam  Khomnei bai yarda da raba siyasa da addini ba, domin kuwa yana da imanin cewa makomar al’umma tana damfare ne da addininsu, kamar yadda kuma siyasa ita ce tafiyar da lamurran rayuwarsu da sha’anin mulki, wanda addini kuma yana da tsari da ya tanadar domin tafiyar da al’umma wanda shi ne siyasa.

A kan haka Imam ya kalubalanci sarakuna na lokacinsa wadanda suka mika kasar Iran ga turawa, kuma suka mayar da salon rayuwar jama’a irin na turai, wanda ya sabawa koyarwa ta addinin da suka yi imani da ita  a matsayinsu na musulmi.

Daga cikin bakin da za su halarta akwai wasu daga Syria, sai kuma wasu kasashen yankin, inda mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kasem yana daga cikin wadanda za su gabatar da jawabi.

Dr. Hakham Yunus Hamami Lalezar shugaban majami’ar yahudawa a Iran, da kuma shugaban mabiya addinin kirista a kasar gami da sauran banagrori marasa rinjayea  kasar za su halarci wurin tare da gabatar da jawabai.

3975041

 

captcha