IQNA

Jagoran Juyi Na Iran: Ilimi Da Hikima Da Basira Da Dogaro Da Allah Su Ne Mabudin Nasara Ga Imam Khomeini

23:51 - June 04, 2021
Lambar Labari: 3485983
Tehran (IQNA) Jagoran juyin juya halin muslunci na Iran ya bayyana cewa, dukkanin matsin lambar da makiya kasar Iran suke yi a kanta ba su iya durkusar da ita ba.

A lokacin da yake gabatar da jawabi a yau dangane da cikar shekaru 32 da rasuwar marigayi Imam Khomeini, Jagoran juyin juya halin muslunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa, tsawon shekaru 42 da samun nasarar juyin juya halin musulunci a kasar, tun daga lokacin kasar take fuskantar matsin lamba da nufin ganin bayanta, wanda hakan bai yi nasara ba.

Jagoran ya ce, akwai abubuwa biyu da marigayi Imam Khomeini ya yi amfani da su wadanda suka baiwa juyin damar wanzuwa, sabanin sauran juyin juya halin da aka yi a wasu kasashe wadanda suka rushe ba da jimawa ba.

Ya ce Kalmar Jamhuriya da kuma muslunci, wadanda su ke nufin riko da koyarwa ta addini, da kuma bai jama’a damar su zama bangare ne na gudanar da lamarin mulkinsu da gwamnatinsu, wanda wadannan abubuwa biyu ne babban sirrin wanzuwar tsarin kasar.

Ya ce babban lamari kuma wanda shi ne tun farko ya gishikin nasara, shi yin amfani da ilimi da kaifin basira da zurfin tunani da hikima da hangen nesa irin na Imam Khomeini, babban makamin da ya yi riko da shi kuma wajen samun nasara ta karshe shi ne dogaro da Allah madaukakin sarki.

Haka nan kuma ya tabo batun zaben da ke tafe a kasar, inda ya jaddada wajabcin fitowar jama’a baki daya kwansu da kwarkwatarsu domin kada kuri’unsu, da kuma yin dogon nazari dangane da wanda za su kada wa kuri’a.

Dangane da ‘yan takara kuma ya jahankalinsu da cewa, bai halasta ba su yi al’umma alkawullan da ba za su iya cikawa ba, domin hakan bai halasta ba a addinin muslunci, sannan kuma yana cutar da kasa da kuma tsarinta.

 

3975570

 

captcha