IQNA

Allah Ya Yi Wa Limamin Babban Masallacin Sayyida Zainab Da Ke Birnin Alkahira Rasuwa

23:51 - June 07, 2021
Lambar Labari: 3485990
Tehran (IQNA) Allah ya yi wa limamin masallacin sayyida Zainab da ke birnin Alkahira na kasar Masar rasuwa sakamakon hadarin mota.

Tashar akhbar Alyaum ta bayar da rahoton cewa, a daren jiya Lahadi Allah ya yi wa Sheikh Abdullah al-azb limamin masallacin sayyida Zainab da ke birnin Alkahira na kasar Masar rasuwa sakamakon hadarin mota a kan hanyarsa ta komawa gida, bayan kammala sallar Isha'i a masallaci.

Sheikh Abdullah Al-azb dai ya shahara da shirinsa da yake gabatar da karatun kur'ani a tashar talabijin da dmc ta kasar Masar.

Malamai daban-daban a kasar ta Masar sun fitar da bayanai na yin ta'aziyyar rasuwarsa tare da nuna juyayi kan wannan babban rashi da aka yi.

Masu hidima a cibiyar Sayyida Zainab da kuma masallacin cibiyar sun bayyana malamin da cewa mutum ne mai yawan ibada da mayar da hankali ga lamarin kur'ani, kamar yadda kuma ya kasance mai shiga gaba a kowane lokaci a wajen bukatun jama'a tare da taimaka musu.

 

3975865

 

captcha