Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, sheikh Muhammad Bin Abdulkarim Isa babban sakataren kungiyar kungiyar hadin kan duniya musulmi ya fitar da bayani, wanda a cikinsa ya yi Allawadai da kakkausar murya kan harin ta’addancin da aka kai wa musulmi a kasar Canada.
Sheikh Muhammad ya ce, wannan hari na ta’addanci ne wanda ba shi da banbanci da sauran hare-hare da ake kaiwa kan wadanda ba su ji ba su gani ba, da sunan kowace irin akida.
Ya ci gaba da cewa, suna yin kira a kan wajabcin daukar matakai na kare rayukan msuulmi marassa rinjaye a kasashen turai, domin kauc wa sake faruwar irin haka.
A ranar Lahadi da ta gabata ce da dare, wani matashi da ke tuka wata mota, ya kai hari da motar a kan wasu musulmi iyalan gida guda, inda ya kashe hudu daga cikinsu, yayin da wani karamin yaro kuma ya samu munanan raunuka, wanda ake kula da shi yanzu a asibiti.