IQNA

Mahardata Kur'ani 'Yan Kasar Ghana Sun Nuna Kwazo A Gasar Hardar Kur'ani Ta Yanar Gizo

23:46 - June 11, 2021
Lambar Labari: 3486002
Tehran (IQNA) mahardata kur'ani 'yan kasar Ghana suna nuna kwazo a gasar hardar kur'ani ta yanar gizo

Jaridar Graphic Ghana ta kasar Ghana ta bayar da rahoton cewa, mahardata kur'ani 'yan kasar Ghana suna nuna kwazo a gasar hardar kur'ani ta yanar gizo, wadda cibiyar sarki Muhammad na shida na Morocco ta dauki nauyin shiryawa.

Sheikh Mustafa Ibrahim shi ne mai kula da wannan cibiya ta sarkin Morocco a reshenta da ke kasar Ghana, wanda kuam cibiya ce da ke kula da lamarrun addini a nahiyar afirka.

A yayin wannan gasa da aka gudanar ta hanyar yanar gizo, mahardata kur'ani daga kasashe daban-daban na Afirka sun shiga gasar, amma wadanda suak zo na daya da na biyu da na uku dukkaninsu 'yan kasar Ghana ne.

An bayan bayar da kyautuka na musamman ga dukkanin wadanda suka nuna kwazo, daga ciki har da kyautar dala dubu 6 da aka raba wa wadanda suka zo na daya da na biyu da na uku.

 

3976784

 

captcha