Tehran (IQNA) An fitar da hoton bidiyo na sabon karatun Mahmoud Shahat Anwar, shahararren mai karatu dan kasar Masar, inda ya karanta suratu Ghashiyyah da Al-Ala, a yanar gizo.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an gudanar da wannan karatu ne a ranar 22 ga watan Yuli a kauyen Nasseriya na lardin Damietta na kasar Masar, kuma mazauna kauyen Nasseriya ne suka halarci wannan biki.