A cewar Amed, mutane da dama ne suka kai hari a masallacin al-Aqsa a yau, Litinin, karkashin kariyar 'yan sandan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.
Ma'aikatar Dokokin Musulunci a birnin Quds ta bayar da rahoton cewa, a harabar masallacin Al-Aqsa, an ga yadda gungun 'yan kaka-gida ke kwararowa daga wajen Bab al-Maghrabh, inda suka gudanar da tarukan Talmud, da aiwatar da ayyukan tunzura jama'a, da kuma sauraren bayani kan abin da suke kira da haikali.