IQNA

Gabatar da abubuwa masu jan hankali na Musulunci a cikin harsuna 25 don masu yawon bude ido a Turkiyya

16:51 - August 16, 2022
Lambar Labari: 3487697
Tehran (IQNA) Ibrahim Tash Demir, limamin kasar Turkiyya mai wa'azi a masallacin Isa Bey ya gabatar da ayyukan addinin musulunci cikin harsuna 25 ga masu yawon bude ido na yankin Seljuk da ke lardin Izmir na kasar Turkiyya.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Anatoly cewa, ‘yan yawon bude ido na kasar Turkiyya sun yi maraba da shirin Ibrahim Tash Demir na kasar Turkiyya na gabatar da al’adun addinin musulunci ga masu yawon bude ido daga sassa daban-daban na duniya a masallacin Issa Bey da ke yankin Seljuk na lardin Izmir na kasar Turkiyya. An gina wannan masallaci a shekara ta 1375 miladiyya.

Wannan limamin kasar Turkiyya ya kwashe shekaru 7 yana karbar baki 'yan kasashen waje masu yawon bude ido a masallacin Issa Bey mai tarihi da ke yammacin Izmir tare da kamshi na tsiro da turare.

Bayan ya san masu yawon bude ido, yana magana da yarensu na asali, an ce yana iya magana da harsuna 25 daban-daban da suka hada da Larabci, Ingilishi, Faransanci, Jamusanci da Fotigal.

Bayan tattaunawa da wadannan ’yan yawon bude ido, Tash Demir ya ba su kasidu da suka shafi ibada da koyarwar Musulunci da kuma hakuri da ‘yan uwantakar addini a Musulunci. Har ila yau, wannan limamin dan kasar Turkiyya ya mika masa kwafin tarjamar kur'ani mai tsarki, wanda yake cikin harshen uwa na kowane dan yawon bude ido.

Tash Demir ya bayyana a cikin wata hira da manema labarai: yin magana a cikin harshen uwa na masu yawon bude ido yana ba su fahimtar tsaro da amincewa. A cewarsa, wasu daga cikin wadannan ‘yan yawon bude ido sun musulunta bayan sun gana da shi kuma har yanzu suna hulda da shi bayan shekaru masu yawa.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4078315

 

captcha