IQNA

Kwanakin Karshen Baje kolin kur'ani na Tehran

IQNA – A yau 2 ga watan Afrilu ne za a kammala baje kolin kur’ani mai tsarki na kasa da kasa karo na 31 a birnin Tehran, wanda ake ci gaba da gudanar da shi a dakin sallah na Imam Khumaini (RA) tun ranar 22 ga watan Maris.

Ma'aikatar al'adu da shiryarwar muslunci ce ke shirya baje kolin duk shekara a cikin watan Ramadan da nufin inganta fahimtar kur'ani da raya ayyukan kur'ani.