IQNA

Sakon Sabuwar Shekara Na Daesh Kan Lasisin Shiga Aljannah

22:12 - December 30, 2017
Lambar Labari: 3482253
Bangaren kasa da kasa, ‘yan ta’addan daesh sun fitar da wani bayani da ke bayyana cewa akwa lamunin shiga aljanna a lokacin kirsimati shi kashe duk wanda ba musulmi ba.

Kamfanin dillacin labaran iqna ya habarta cewa, shafin fronpagemag ya bayar da rahoton cewa, ‘yan ta’addan daesh sun fitar da wani bayani na faifan bidiyo da ake nuna wani dan ta’adda rike da wani dattijo sanye da kayan kirsimati, inda yake bayyana cewa akwai lamunin shiga aljanna a lokacin kirsimati shi kashe duk wanda ba musulmi ba a duk inda aa same shi.

Inda ya karanto wani wani hadisi da ya danganta da manzon Allah (SAW) inda ya ce manzon Allah ya ce; kafiri da wanda ya kashe shi ba za su hadu a jahannama ba.

Yana mai yin ishara da hakan a matsayin lasisin shiga aljanna ga duk wanda ya kashe wanda ba musulmi, bisa hujjar cewa kafiri zai tafi wuta, shi kuma ya kashe ba zai taba shiga wuta ba.

Mutumin wanda ya rufe fuskarsa da bakin kyalle ya bayyana cewa, matukar dai tutar musulunci mai dauke da Kalmar shahada bata filfila a duniya ba, to za su ci gaba kashe kafurai.

‘Yan ta’adda suna yin amfani da hadisan da aka kirkiro bayan manzon Allah da kuma hadisai na gaskiya da suke karkata fassararsu zuwa ransu, domin aikata ta’addanci da bata sunan addinin musluncia  idon duniya.

3677419

 

 

 

captcha