IQNA - Daga ranar 22 ga watan Yulin shekarar 2025 ne aka fara gudanar da bukin "Birnin Muharram" karo na uku na shekara shekara, wanda zai gudana har zuwa ranar 5 ga watan Agusta a dandalin Azadi da ke birnin Tehran.
IQNA - Kungiyar masu fafutukar kur’ani ta kasar Iran ta gana da iyalan Laftanar Janar Hossein Salami, marigayi kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci tare da girmama tunawa da wannan makarancin kur’ani mai tsarki da ya yi shahada.
IQNA- An fara gudanar da gasar kur'ani mai tsarki ta kasar Iran karo na 48 a safiyar yau Juma'a 25 ga watan Yulin 2025 a karkashin kulawar ma'aikatar kula da ayyukan jin kai ta lardin Tehran a Otel Eram.
Aa ranar 26 ga watan Yulin shekara ta 2025 ne aka gudanar da bikin baje koli a hubbaren Imam Khumaini dake kudancin birnin Tehran na kungiyar agaji ta Red Crescent ta Iran (IRCS) da suka nufi kasar Iraki domin gudanar da tarukan ziyarar Arbaeen.