IQNA

Saudiyya Ta Amince Da Bude Masallacin Ma’aiki (SAW) Mataki-Mataki

22:57 - May 30, 2020
Lambar Labari: 3484849
Tehran (IQNA) gwamnatin kasar saudiyya ta amince kan bude masallacin ma’aiki (SAW) mataki-mataki.

Sarkin kasar Saudiyya ya amince da a bude masallacin manzon Allah (SAW) mataki-mataki daga ranar gobe Lahadi ga masallata.

Gidan talabijin kasar Saudiyya ya bayar da rahoton cewa, saki kasar ya amince da hakan ne bisa shawara ta jami’an kiwon lafiya, inda ya bayyana cewa dole ne a kiyaye dukkanin umarninsu dangane da wannan batu.

Yanzu haka dai ana ci gaba da yin feshi a ciki da wajen masallacin domin kashe kwayoyin cuta, tun bayan bullar cutar corona ne dai aka saka dokar hana yin sallali a cikin masallacin ma’aika da na Makka.

Manufar hakan dai ita ce tabbatar da cewa an dakile yaduwar cutar corona a kasar, wanda hakan ya hada da daukar matakai na hana taruka da kuma bayar da tazara.

Muhammad Abdul’al kakakin ma’aikaatar kiwon lafiya na kasar ya bayyana cewa, ya zuwa mutane 76,726 ne suka kamu da cutar, yayin da 411 suka rasa rayukansu, 48,450 kuma suka warke.

 

3901831

 

captcha