IQNA

MDD Ta Yi Allawadai Da Kona Kur'ani A Sweden

21:00 - August 31, 2020
Lambar Labari: 3485138
Tehran (IQNA) Majalisar dinkin duniya ta yi Allawadai da kona kwafin kur’ani mai tsarki a kasar Sweden.

Majalisar dinkin duniya ta yi Allawadai da kakkausar murya kan kona kwafin kur’ani mai tsarki da masu tsatsauran ra’ayin kyamar addinin musulunci suka yi a kasar Sweden.

Shugaban kwamitin kula da harkokin addinai na majalisar dinkin duniya Miguel Moratinos ya bayyana kone kwafin kur’ani mai tsarki da wasu masu tsananin kiyayya da musulunci suka yi a kasar Sweden da cewa abin yin tir da Allawadai ne.

Ya ce kur’ani littafi ne daga littafai masu tsarki na mabiya addinai da aka saukar daga sama, wanda abin girmamawa ne ga daukacin musulmi, saboda haka keta alfarmar wannan littafi na a matsayin keta alfarmar dukkanin musulmi ne, da ma sauran addinai.

A kan haka ya wannan ba abu ne da za a lamunta da shi ba, dole ne mahukunta da sauran masu fada a ji da suka hada da malamai da jagorori na mabiya addinai su tsawata wa mabiyansu kan wajabcin girmama sauran addinai, da nisantar duk wani abu na cin zarafi ko keta alfarmar wani abu mai tsarki a cikin wani addini.

3919989

 

captcha