Shafin yada labarai Sada ya bayar da rahoton cewa, babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi Muhammad Al-Isa ya mayarwa Macron da martani da cewa, addinin musulunci sako ne na ubangiji, wanda babu wani abu na kaucewa a cikinsa.
Ya ce babu mai musu kan cewa akwai wasu daga cikin musulmi da suke fahimtar addini a birkice, wanda hakan ne ke kais u ga aikata ayyukan ta’addanci da sunan addini, amma ba addinin ne ya koyar da su ta’addanci, domin kuwa babu ta’addanci a cikin addinin musulunci.
Ya ci gaba da cewa, ba adalci ba ne a yanke hukunci a kan addinin musulunci da ayyukan da wasu masu tsatsauran ra’ayi da da ba su fahimci koyarwar musulunci ba, domin kuwa a cikin kowane addini ana samun hakan, kuma adalci ba ne a hukunta kowane addini da ayyukan irin wadannan mutane.
A cikin ‘yan kwanakin nan ne dai shuban kasar ta Faransa yay i kalamai na nuna kyama ga musulmi, tare da bayyana su a matsayin babban hadari ga makomar kasar Faransa saboda ayyukan ta’addanci.