IQNA

Masallacin Al-Kutubiyyah Yana Daga Cikin Masallatan Tarihi A Afirka

Tehran (IQNA) masallacin Al-kutubiyyah da ke kasar Morocco yana daga cikin masallatai na tarihi a nahiyar Afirka.

An gina wannan masallacin nea  birnin Tabat a lokacin daular Almuwahidin, inda Khalifah Abdulmumin Bin Ali Alkumi ya bayar da umanin gina masallacina  cikin shekara ta 1158 miladiyya, kimanin shekaru dari tara da suka gabata, inda aka gina masallacin da tulluwa 17, kuma tun daga karni na 12 har yanzu ana amfani da masallacin.