IQNA

Jagoran Juyi A Iran:

Shekarar 1400 Hijira Shamsiyya: Shekarar Кere-ƙere Goyon Baya Da Kawar Da Cikas

11:55 - March 21, 2021
Lambar Labari: 3485758
Tehran (IQNA) Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei ya ska wa Shekarar 1400 Hijira Shamsiyya: Shekarar Кere-ƙere Goyon Baya Da Kawar Da Cikas.

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya taya al’ummar Iran da sauran al’ummomin da suke gudanar da bukukuwan sabuwar shekara ta hijira shamsiyya da ake kira da Nowruz yana mai kiran jami’an gwamnatin ƙasar da su ba da himma wajen ƙarfafa ƙere-ƙere da kuma kawar da duk wani abin da zai kawo cikas ga hakan.

Jagoran ya bayyana hakan ne cikin wani jawabi da yayi wa al’ummar ƙasar ta kafafen watsa labarai na na radiyo da talabijin don taya al’umma shigowar sabuwar shekara ta hijira shamsiyya ta 1400 da ta faɗo da tsakar ranar yau ɗin nan Asabar inda ya jinjinawa wa al’ummar Iran ɗin saboda tsayin dakan da suka yi wajen tinƙarar irin ƙalubalen da suka fuskanta cikin shekara ta 1399 da gabata da suka haɗa da annobar nan ta Coronavirus da kuma takunkumi da matsin lamba daban-daban da suka fuskanta daga wajen maƙiya.

Jagoran ya yaba wa likitoci da malaman jiyya daban-daban na ƙasar dangane da irin namijin ƙoƙarin da suka yi wajen tinƙarar annobar ta Coronavirus kamar yadda kuma ya isar da saƙon ta’aziyya da kuma juyayinsu ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon cutar ta Corona.

Dangane da batun matsin lamba da kuma takunkumin da maƙiya suka sanya wa Iran ɗin da kuma shan kashin da suka sha a wannan ɓangaren, Jagoran ya ce su da kansu maƙiyan Iran ɗin suna tabbatar da cewa waɗannan matsin lamba ta su akan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sha ƙasa.

Daga ƙarshe dai Imam Khamenei ya sanya wa sabuwar shekarar ta 1400 sunan shekarar: Кere-ƙere: Goyon Baya Da Kuma Kawar Da Cikas, yana mai kiran jami’ai da al’ummar ƙasar da su zage damtse wajen ganin an cimma wannan manufar da aka sanya a gaba.

3960726

 

 

 

 

 

 

 

 

captcha