IQNA

Hamas: Sakin Abu Atwan Nasara Ga Gwagwarmayar Falasinawa

21:56 - July 09, 2021
Lambar Labari: 3486088
Tehran (IQNA) kungiyar Hamas ta bayyana sakin Abu Atwan da Isra'ila ta yi ala tilas, hakan babbar nasara ce ga gwagwarmayar Falastinawa.

A rahoton kamfanin dillancin labaran iqna, a jiya ne Isra’ila ta saki Gadanfar Abu Atwan, wanda ya kwashe tsawon kwanaki 65 yana yajin cin abinci.

Abu Atwan ya yi nasara wajen tilasta Isra’ila ta sake, sakamkon tsare shi da take yi ba tare da wani laifi ba, ta hanyar shiga yajin cin abinci, lamarin da ya daga hankulan hukumomin yahudawa.

A yayin zantawarsa da Almayadeen Abu Atwan ya jaddada cewa, sakinsa ba zai hana shi ci gaba da gwagwarmaya da zalunci da kuma mamayar Isra’ila a kan yankunan Falastinawa ba, inda ya ce yanzu ne ya fara wannan gwagwarmaya ta neaman 'yanci har zuwa lokacin ‘yantar da Falastinu daga mamayar yahudawa.

Bayan kwashe tsawon kwanaki fiye da hamsin yana yajin cin abinci, Abu Atwan ya shiga yajin cin abinci har da ruwan sha, wanda hakan yasa rayuwarsa ta shiga cikin hadari a cikin makon nan, inda a jiya Isra’ila ta sanar da cewa ta sake shi.

Yanzu haka dai yana kwance a asibiti ana kula da lafiyarsa, bayan da jikinsa ya yi rauni matuka, ta yadda ba zai iya ko tsayawa a kan kafafunsa ba sai dai a kan keken turawa.

 

3982844

 

 

captcha