IQNA

Musulmin Canada Sun Yi Marhabin Da Matakin Hukunta Masu Cutar Da Mutane Saboda Addini

22:26 - August 12, 2021
Lambar Labari: 3486196
Tehran (IQNA) musulmin birnin Edmonton na Canada sun yi lale marhabin da matakin hukunci na doka a kan masu cutar da mutane saboda dalilai na addini.

Tashar CNN ta bayar da rahoton cewa, musulmin birnin Edmonton na kasar Canada sun yi lale marhabin da matakin hukunci na doka a kan masu cutar da mutane saboda dalilai na addini wanda gwamnatin jihar ta fitar.

Rahoton ya ce, tun kafin wannan lokacin majalisar dokokin jihar ta taba kafa irin wannan doka amma daga bisani aka jingine yin aiki da ita.

A halin yanzu wasu daga cikin 'yan majalisar dokokin sun sake gabatar da wani kudiri da ke neman a sake dawo da yin aiki da wannan doka.

Yanzu haka an sanya ranar Litinin mai zuwa ta zama tattauna wanann kudiri, da kuma yanke matsaya guda a kansa, inda ake sa ran galibin 'yan majalisar za su amince da hakan.

Daga cikin matakan da dokar za ta kunsa, duk wanda aka kama shi da laifin cin zarafin wani saboda banbancin addini ko launin fata ko kabila, to zai fuskanci hukunci bisa wanann doka, sannan kuma za a yi masa tara wadda zata fara daga dala dari biyu da hamsin, idan ya kara za a rubanya tarar a kansa.

Musulmin kasar Canada sun yi lale marhabin da hakan tare da yin kira ga 'yan majalisar da su amince a aiwatar da wannan kudiri kamar yadda aka tsara shi.

 

 

3990301

 

 

 

captcha