IQNA

An Gudanar Da Zaman Juyayi A daren Tasu'a Tare Da Halartar Jagoran Juyi Na Iran

20:53 - August 18, 2021
Lambar Labari: 3486217
Tehran (IQNA) an gudanar da zaman juyayia daren Tasu'a a Husainiyar Imam Khomeini tare da halartar jagoran juyi na Iran.

Shafin yada labarai na jagoran juyin juya halin musulunci a Iran ya bayar da bayanin cewa, a daren jiya an gudanar da zaman juyayia daren Tasu'a a Husainiyar Imam Khomeini tare da halartar jagoran juyi na Iran.

Hojjatol Islam Sa'adi ne ya gabatar da jawabi a wurin, inda ya mayar da hankali kan abubuwan da suka faru a ranar Tasu'a ga Imam Hussain (AS) da sahabbansa da kuma zuriyar manzon Allah (SAW) da suke tare da shi, inda ya bayyana tsayin dakan da suka yi a wannan rana shi ne babban sirrin nasararsu a ranar Ashura.

Kamar sauran kwanakin da suka gabata an takaita halartar jama'a a wurin taron, sakamakon matsaloli na kiwon lafiya da ake fama da su a wannan lokaci.

 

3991465

 

captcha