IQNA

Matashi Mai Aikin Fenti Yana Karatun Kur'ani A Lokaci Guda

22:57 - September 18, 2021
Lambar Labari: 3486324
Tehran (IQNA) Yusuf Ahmad Hussain matashi ne da yake aikin fenti kuma yana karatun kur'ani a lokaci guda.

Jaridar yaum Sabi ta bayar da rahoton cewa, Yusuf Ahmad Hussain matashi ne dan kasar Masar da yake aikin fenti kuma yana karatun kur'ani a lokaci guda da sautin karatun mai natsar da zuciya.

Yusuf ya tashi a gidan mutane masu karatun kur'ani dukkanin iyalan gidan sun hardace kur'ani baki dayansu, wanda hakan yasa shi ma tun yana karami ya hardace kur'ani cikin sauki.

Ya ce bai sha wata wahala ba wajen hardar kur'ani mai tsarki, domin abu ne wanda yake ji kullum rana ana yi, saboda haka ya hardace kur'ani saboda yawan karatun da yake yi.

Daga bisani bayan klammala karatun sakandare ya tafi jami'a inda ya yi digiri a kan ilimin koyarwa, amma kuma a lokaci guda yana sha'awar aikin fenti.

a kan haka ya ci gaba da yin aikin fenti da kuma koyarwa, kamar yadda kuma ya shahara da karatun kur'ania  duk lokacin da yake aiki, wanda hakan yasa mutane suke jin dakin aikinsa.

 

 

 

3998172

 

 

captcha