IQNA

An Buga rahoton Kungiyar Musulunci ta Canada a jajibirin ranar yaki da kyamar Musulunci ta kasa

22:22 - January 27, 2022
Lambar Labari: 3486876
Tehran (IQNA) Wata kungiyar Musulunci ta fitar da wani sabon rahoto kan kyamar Musulunci a cikin rayuwar Musulman kasar Canada ta yau da kullum.

Kungiyar agaji ta Islamic Relief Organisation ta kasar Canada a yau ta fitar da wani sabon rahoto da ke nuna yadda kyamar Musulunci ta yau da kullum ke shafar musulman kasar Canada.

An buga wannan rahoto ne a jajibirin cika shekaru biyar da harbe-harbe a masallacin Quebec da kuma ranar yaki da kyamar Musulunci ta kasa.

Rihanna Patel, daraktan hulda da jama'a a gwanatin Canada ta ce "Muna yawan jin labarin kyamar addinin Islama a cikin mahallin da musulmi ke rayuwa, da munanan hare-hare, amma abin da ba a sani ba shi ne al'amuran yau da kullun da kuma kananan cin zarafi da Musulmai ke fuskanta a kai a kai a kowane bangare na rayuwa," in ji Rihanna Patel, daraktan hulda da jama'a ta gwamnatin Canada.

Ta ce muna daukar dukkanin matakan da suka dace domin shiga kafar wando daya da masu nuna kyama ga musulmi a fadin Canada, kamar yadda kuma duk wandfa aka samu da irin wannan laifi tabbas zai gurfana a gaban shari'a domin hukunta shi.

 

 

 

 

 

4031849

 

captcha