Kamfanin dillancin labaran anatoli ya bayar da rahoton cewa, mutane da dama ne 'yan kasar da mazauna birnin Istanbul ne suka hallara a masallatan Chamlija, Hagia Sophia da Ayub Sultan da ke Istanbul a yammacin ranar Alhamis 5 ga watan Fabrairu, inda suka halarci bikin Laylat al-Raghaib.
Hukumar kula da harkokin addini ta Turkiyya ( Religion Organization) da kuma Istanbul Dar al-Afta sun gudanar da wani shiri na addini a babban masallacin Ayub Sultan.
A cikin wannan shiri na addini, yayin da ake karanto ayoyin kur'ani mai tsarki da addu'o'i na musamman na wannan dare, an kuma gabatar da Tawashih da Ibtihal.
Baya ga wannan masallacin, an kuma gudanar da wasu shirye-shirye na addini a wasu masallatan Istanbul, da kuma sauran masallatan kasar Turkiyya, a daidai daren Juma'a na farko na watan Rajab.
https://iqna.ir/fa/news/4033692