IQNA

Wani Mai Fasahar Rubutu A Pakistan Ya Rubuta Dukkanin Kur’ani A Kan Fensir

16:46 - April 07, 2022
Lambar Labari: 3487138
Tehran (IQNA) Wani mai fasaha dan kasar Pakistan ya rubuta dukkan ayoyin kur'ani mai tsarki a kan fensira 8,000 a hanya ta musamman mai ban sha'awa aikin da ya dauke shi tsawon shekaru 10.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Aljazeera ya bayar da rahoton cewa, Shah Nawaz Malhi, wani jami’in ‘yan sandan Pakistan ne mai ritaya, wanda ya yi nasarar rubuta dukkan surori 114 na kur’ani ta hanyar amfani da fensir  guda 8,000.

Adadin fensiran da aka yi amfani da su a kowace surah ya bambanta gwargwadon tsawon surorin, wanda ya kai daga 50 zuwa 70 har ma da fensir 100 zuwa 500.

Shah Nawaz Malhi ya makala fensin a jikin allo ta hanyar amfani da faifan robobi sannan ya sanya sunan kowace surah a cikin wani firam na musamman a kan allo, wanda wannan aikin fasaha ne na musamman, kuma a yanzu  yana daya daga cikin abubuwan nunawa a duniya.

Ya ce "Na yi ritaya daga aikin 'yan sanda a Pakistan a shekara ta 2014, kuma ni ne Hermandi na farko da ya saƙa dukkan ayoyin kur'ani ta hanyar amfani da zare akan fensir," in ji mai zanen dan Pakistan.

Ya kara da cewa: “Aikin fasaha na burge ni tun ina makarantar firamare, kuma wannan sha’awar ta karu a gare ni, kuma a shekarar 2002 na samu damar rubuta ‘Asmaullah al-Husna’ da rubutun larabci, na nuna shi a majalisar fasaha ta Karachi da ke Pakistan.

Shah Nawaz Malhi ya ce, “Na yi aiki tukuru na tsawon shekaru 10,  sa’o’i 8 a kowace  rana don samun damar saka dukkan ayoyin kur’ani a kan fensir, tare da taimakon ‘yan uwa da abokan arziki.

ابتکار هنرمند پاکستانی در بافت کل قرآن بر روی مداد

ابتکار هنرمند پاکستانی در بافت کل قرآن بر روی مداد

ابتکار هنرمند پاکستانی در بافت کل قرآن بر روی مداد

ابتکار هنرمند پاکستانی در بافت کل قرآن بر روی مداد

ابتکار هنرمند پاکستانی در بافت کل قرآن بر روی مداد

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4047540

 

 

 

 

captcha