IQNA

Amincewa da kai wajen fuskantar kalubale ga mace mai saka lullubi

15:57 - May 01, 2023
Lambar Labari: 3489070
Tehran (IQNA) Nasarar da "Hayat Sindi" ta samu ta nuna cewa ta iya kalubalantar ra'ayoyin da ke da alaka da matan musulmi a Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, a cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan, tare da samun ci gaba da bunkasuwar fasahohin zamani, lamarin ilimi da ci gaba a fannoni daban-daban ya sa mata sun samu sauki ta bangarori daban-daban.

Duk da cewa har yanzu mata a mafi yawan sassan duniya na fama da rashin daidaito kamar biyan albashi da kuma matsalolin samun damar shiga kasuwannin da suka dace, yanayin da ake ciki a kasashe daban-daban ya nuna irin ci gaban da mata ke samu a kasuwar kwadago da kuma rawar da suke takawa a fannin kimiyya.

A kasashen musulmi, lamarin ya dan bambanta. Batutuwa na son zuciya da wasu kan danganta su da addini da kuma al’adu na gargajiya da kuma rashin kimanta mata, ya sa matan musulmi ba su da yawa a fagen ilimi da bincike a fagage daban-daban. Wannan kuwa duk da cewa Musulunci bai haramta ilimin ga mata ba.

Hayat Sindi, an haife ta ne a ranar 6 ga watan Nuwamba, 1967, ‘yar kasar Saudiyya ce scientist, kuma daya daga cikin mata na farko a majalisar tuntuba ta kasar Saudiyya, wadda ta iya kalubalantar ra’ayoyin da ake dangantawa da mata musulmi a kasarta. Tana daya daga cikin sanannun masana kimiyyar likitanci a yankin.

Binciken da ta yi a fagen kimiyyar halittu, wanda aka sani a duniya, ya tabbatar da kyakkyawan suna a gare ta; Duka a matsayin mai ba da shawara kan samar da magani mai araha kuma a matsayin mai ba da taimako.

 

4136481

 

captcha