IQNA

Fitattun Mutane A Morocco Sun Sanya Hannu Kan Takardar Yin Allawadai Da Kulla Alaka Da Isra’ila

23:22 - December 18, 2020
Lambar Labari: 3485471
Tehran (IQNA) wasu daga cikin fitattun mutane a kasar Morocco sun sanya hannu kan takardar yin Allawadai da kulla alaka da Isra’ila da kasar ta yi.

Jaridar Quds Al-arabi ta bayar da rahoton cewa, a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da wasu daga cikin fitattun mutane a kasar Morocco suka sanya hannu a kanta, sun yin tir da Allawadai da kulla alaka da Isra’ila da kasar ta yi.

Bayanin ya kunshi sanya hannu daga fitattun mutane a kasar ta Morocco, da suka hada da manyan malamai a kasar, da kuma manyan lauyoyi, gami da wasu daga cikin manyan ‘yan siyasa, da kuma jagororin kungiyoyin farar hula a kasar.

Daga cikin abin bayanin ya kunsa, har da yin Allawadai da matakin da sarkin kasar ta Morocco ya dauka na sanar da kulla alaka da Isra’ila ba tare da izinin al’ummar kasar ko neman jin ra’ayinsu kan haka ba, duk kuwa da cewa ya san matsayin al’ummar Morocco kan cewa ba za su taba amincewa da Isra’ila  a matsayin kasaa cikin Falastinu ba.

Bayanin fitattun mutane kasar ta Moroo ya kiayi sarkin kasar da ya gaggauta janye batun kulla hulda da gwamnatin yahudawan Isra’ila, idan kuma bah aka ba, al’ummar Morocco za ta kalli hakan a matsayin cin amanar al’ummar Falastinu da larabawa da ma musulmi ba baki daya.

A ranar Alhamis da ta gabata ce a karkashin matsin lambar Amurka da Saudiya, sarkin Morocco ya sanar da kulla alaka tsakanin kasarsa da kuma gwamnatin yahudawan Isra’ila.

 

3941723

 

captcha