IQNA

Masallaci Mafi Girma A Nahiyar Afirka Na Da Abubuwa Da Suka Banbambanta Shi Da Sauran Masallatai

23:00 - June 01, 2021
Lambar Labari: 3485972
Tehran (IQNA) babban masallacin kasar Aljeriya shi ne masallaci mafi girma a dukkanin nahiyar Afirka da ke daukar masallata dubu 120 a cikinsa.

Babban masallacin kasar Aljeriya wanda shi ne masallaci mafi girma a duniya, an bude shi ne a ranr 18 ga watan Oktoban 2020,a  lokacin maulidin manzon Allah (SAW).

Masallacin yana fadi mita dubu 377, da hakan ya hada dukkanin bangarorinsa, baya ga wurin da ake yin salla, da kuma makekeyar haraba, akwai bangarori daban-daban a cikinsa. 

Daga cikin wurare akwai makaranta da cibiyar bincike na ilimi, wanda za a iya koyar da daruruwan dalibai a lokaci guda.

Baya ga haka kuma akwai wuri na musamman da kebe domin dubar jinjirin wata tare da na'urori na zamani da aka tanada.

Hasumiyarsa wannan masalalci ita ce mafi tsawo  fiye da dukkanin hasumiyoyi na masallatai a duniya baki daya, inda hasumiyar tsawonta ya kai mita 265, sannan a cikinta tana da hawa 42..

Wani abu mafi daukar hankali a ginin hasumiyar shi ne, an yi ta ne a tsarin gini irin na gargajiyar ta tsarin ginin Afirka.

نگاهی به معماری چشمگیر بزرگترین مسجد قاره آفریقا + عکس

3974893

captcha