IQNA

Aljeriya Na Zargin Morocco Da Hannu Wajen Haddasa Gobarar Daji A Kasar

22:41 - August 19, 2021
Lambar Labari: 3486220
Tehran (IQNA) Gwamnatin kasar Aljeriya tana zargin cewa akwai hannun kasar Morocco a gobarar dajin da ta auku a kasar.

Kasar Aljeriya, ta sanar da cewa za ta sake duba alakarta da kasar Morocco, bisa zargin Masarautar da hannu a wutar dajin da ke ci gaba da ci a kasar.

mutane da dama ne dai daga ciki har da sojoji suka rasa rayukansu a wutar dajin wacce ta fara ci tun daga ranar tara ga wannan wata na Agusta.

Mahukuntan Alger sun sanar da daukan wannan matakin ne yayin wani taron gaggawa na majalisar koli ta tsaron kasar ranar Laraba, wanda shugaban kasar Abdelmadjid Tebboune, ya halarta.

A cewar sanarwar fadar shugaban kasar, ayyukan kiyaya da Morocco ke aikatawa kan Aljeriya, su ne suka tilasta kwakware alakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma tsaurara matakan bincike na tsaro a iyakokin yamma.

Haka kuma gwamnatin Aljeriya, ta zargi wata kungiyar ‘yan a ware ta ‘yan kabilar Kabili dake da zama a birnin Paris, da kuma wata kungiyar mai kishin islama ta Rashad dake da mazauni a birnin Landon da cinna wutar dajin.

 

 

 

3991777

 

 

 

captcha