IQNA

A Karon Farko Jam’iyyar Masu Kishin Islama Ta Sha Kashi A zaben Morocco

16:52 - September 09, 2021
Lambar Labari: 3486288
Tehran (IQNA) tun bayan da aka fara gudanar da zabuka  akasar Morocco, a karon farko jam’iyyar masu kishin Islama ta sha kashi a zaben ‘yan majalisar kasar.

Bisa ga sakamakon zaben majalisar dokokin da aka gudanar a kasar Morocco a jiya Laraba, jam’iyyar RNI ta lashe kujeru fiye da sauran jam’iyyu a majalisar, biye da ita akwai jam’iyya PAM sannan jam’iyyar PJD ta masu kishin addinin ta sami kujeru 8 a majalisar.

Wannan dai shi ne sakamakon farko na zaben ‘yan majalisar dokokin da aka gudanar a kasar ta Morocco a ranar jiya Laraba.

Jam’iyar RNI wacce wani hamshakin attajiri kuma tsohon ministan noma na kasar, Aziz Akhannouch yake jagoranta ta sami kujeru 97 daga cikin kujeru 395 na majalisar dokokin kasar, biye da ita akwai Jam’iyyar PAM mai kujeru 82 daga nan sai jam’iyyar Istiqlal mai kujeru 78.

Jam’iyyar PJD dai ta sami kujeru 8 ne kacal bayan an kirga kashi 96% na kuri’un da aka kada.

 

 

captcha